ABNA24 : Rahoton jaridar yahudawan ta Yedioth Ahronoth ya ce, bisa la’akari da matsanacin halin da kasar Lebanon ta shiga na matsin tattalin arziki da karancin makamashi, idan Nasrullah ya samu nasara wajen wadata kasar Lebanon da man fetur da dangoginsa, to kuwa tabbas hakan zai bai wa kasar Iran damar shimfida ikonta a kan kasar Lebanon cikin sauki.
A cewar jaridar, idan Iran ta samu wannan damar, to kuwa ta kara samun wata babbar dama ta matsowa kan iyakokin Lebanon da Isra’ila, bayan da ta samu irin wannan damar a cikin kasar, wanda hakan babbar barazana ce ga Isra’ila.
Kasar Lebanon ta shiga matsin tattalin arziki da ma wasu matsaloli na daban sakamakon matsin lambar Amurka, da kuma killace babban bankin kasar tare da hana gudanar da mu’malolinsa na kasa da kasa, da nufin tunzura mutanen kasar a kan kungiyar Hizbullah.
Yanzu haka dai Iran ta aike da wani katafaren jirgin ruwa da yake dauke da miliyoyi litar man fetur da dagoginsa zuwa kasar Lebanon, bayan da kungiyar Hizbullah ta bukaci hakan daga Iran, domin fitar da kasar daga matsalar makamashi.
342/